Isa ga babban shafi
Rayuwata

Rayuwata kashi na 538(Yadda mata za su yi girki ba tare da gurbata muhalli ba)

Wallafawa ranar:

Makamashi wani abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar ma’aurata, musamman yadda mata ke amfani da shi a girke girke. Gawayi, kalanzir, hadi da gas da a yanzu ake amfani da shi, abubuwa ne da mata ke mu'amala da su wajen yin girki toh sai dai bincike ya nuna ba karamar illa sakamakonsu kan haifarwa muhalli ba.

Kalanzir da gas na sahun ababen girkin da ke gurbata muhalli.
Kalanzir da gas na sahun ababen girkin da ke gurbata muhalli. AP - Bruna Prado
Talla

A yunkurin kara ayyukan inganta muhalli da inganta rayuwar mata, ofishin jakadancin kasar Faransa a Najeriya ya kaddamar da masana’anta mai mahimmancin gaske da ake kira Power Stove wadda hukumar aiyukan cigaba na kasar Faransa AFD da kungiyar hadinkan kasashen turai EU suka dauki nauyi.

Wannan masana’anta mai suna Power Stove Factory zai samar da risho na girki wanda akayi amfani da wata sabuwar kimiyya wajen samar da makamshi da ake kira falets da baya fidda hayaki. Kuma wani abun farin ciki shine sama da kashi 50 na ma’aikatan wannan masana’anta mata ne.

Ko wane amfani wannan sabon risho zai yi a irin yanayin nan da duniya ke fama da matsalolin sauyin yanayi? Sai ku biyo mu cikin shirin rayuwata na wannan rana,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.