Isa ga babban shafi
Rayuwata

Yadda mata ke fuskantar kalubalen wariya wajen samar da tsaro

Wallafawa ranar:

Shirin Rayuwata a wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda rashin tsaro, har yanzu ke gigitar da jama’ar kasashen yankin sahel musamman arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.Tarihi ya nuna cewa wadannan yankuna sun shafe fiye da shekaru 15 suna fama da hare-haren ‘yan ta’adda daga Boko Haram zuwa masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da sauran ‘yan kungiyoyi masu rike da makamai.

Mata a Najeriya
Mata a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Gwamnatoci da masu ruwa da tsaki na nunawa mata wariya ko kuma banbanci a tattaunawar da ta shafi yadda za a tabbatar da tsaro a yankunan da suke, watakila saboda hasashen cewa basu da gudunmowar da za su iya bayar wa.

Irin wannan kalubale da mata ke fuskanta shine abinda shirin Rayuwata  na wannan lokaci ya yi duba akai.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Rukayya Abba Kabara....

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.