Rayuwata kashi na 545 (Shirin tallafawa Mata don rage radadin rayuwa a Kaduna)
Wallafawa ranar:
Kunna - 09:57
Matsalar tsadar rayuwa na daya daga cikin manyan abubuwa da suka shafi duniya a halin yanzu, ba Kasashe masu tasowa kadai ba, hatta manya Kasashe masu karfin tattalin arziki, na ji a jikinsu.
Akwai dai dalilai da dama da suka haifar da wannan matsala, kamar yake yake, ya haifar da annoba, haka ma matsalar fari da sauyin yanayi ma sun taka rawa wajen haifawa Kasashe matsalar tsadar rayuwa.
Najeriya, kamar sauran Kasashe masu tasowa na daga cikin jerin kasashen da jama’arsu musamman na yankunan karkara, ke fama da matsalar talauci. Hakan ne ya sanya gwamnatoci a matakai daban daban na kasar, bullo da shirye shiryen tsamo jama’a daga matsalar ta hanyar basu tallafi musamman na kudi.
A kan haka shirin rayuwata ya ziyarci jihohin Kaduna da Bauchi a Najeriya, domin jin irin gajiyar tallafin da mata suka samu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu