Isa ga babban shafi
Rayuwata

Rayuwata kashi na 815: Ta'aziyyar Mahamane Salissou Hamissou

Wallafawa ranar:

A cikin Shirin rayuwata na wannan rana wanda Zainab ibrahim ta saba kawo muku za ku ji yadda abokin aiki marigayi moh salisu ya shirya mana rahoto dangane da yadda al’adar tafiye tafiye dan cirani a baya ta fi armashi wajen taimakawa alumma da kasashe masu tasowa irin najeriya da jamhuriyar nijar, wanda a yau an wayi gari al’amari ya canza zani, lura da matsalolin tattalin arziki da na tsaro da duniya ke fuskanta.

Salissou Hamissou a yayin gabatar da labaran duniya
Salissou Hamissou a yayin gabatar da labaran duniya © RFI/ FMM
Talla

Kafin rasuwarsa marigayi Mahamane Salissou Hamissou, ya duba yadda a irin wannan yanayi yara kan taso babu sanayya tsakaninsu da ubannensu, sannan duk namijin kokarin da uwaye ke yi domin tarbiyantar da su, sau da dama a kan samu cikas, bayaga haka su kansu matan kan bukaci taimakon mazajen a lokuta da dama wajen tafiyar da harkokin rayuwa, toh amma kash! Tafiya cirani da mazajen ke yi na tsawon lokaci kan haifar da babban kalubale tsakanin iyalai. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.