Isa ga babban shafi
Shirye-shirye na Musamman

Manyan abubuwan da suka faru a duniya a 2022

Wallafawa ranar:

A yayin da duniya ta yi ban-kwana da shekarar 2022 da ta gabata, Sashen Hausa na RFI ya yi takaitacciyar waiwaya kan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka wakana a bara a matakin kasa da kasa, kama daga rikicin Ukraine har zuwa Gasar Cin Kofin Duniya da Argentinaa ta lashe a Qatar.

Yakin Ukraine ya wujijjiga duniya baki-daya
Yakin Ukraine ya wujijjiga duniya baki-daya © Libkos / AP
Talla

Da sanyin safiyar ranar 24 ga watan Fabairu, sojojin Rasha da suka kwashe tsawon watanni girke a kan iyakar arewacin Ukraine suka kaddamar da yakin neman mamaye kasar a bisa umarnin shugaba Vladimir Putin.

Sa’o’i bayan kadddamar da wannan gagaumin yaki, shugabannin kasashen duniya suka fara mayar da martani ga Putin kan matakin, yayin da wannan yakin ya girgiza duniya baki-daya ta hanyar haddasa tsadar kayayyakin abinci daa kuma kaarayar tattalin arziki da har yanzu ake shan radadinsa a sassan duniya.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.