Kan matsalar ambaliyar ruwa a sassan Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 15:25
Jihohin Najeriya da dama na fama da ibtila’in ambaliyar ruwa wadda ta cinye garuruwa da kauyuka musamman a yankin arewacin kasar, yayin da aka samu asarar rayuka da dimbin dukiya.
Ambaliyar ta lalata gonaki akalla dubu 14 a jihar Kano kadai, yayin da ta cinye filayen noman shinkafa da fadinsu ya kai kilomita 250 a jihar Taraba, baya ga irin baarnar da ta ke ci gaba da yi a jihohin Yobe da Nasarawa da Adamawa da Bauchi da Lagos da dai saurannsu.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin da Hauwa Muhammad ta shirya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu