Kan tayin da Aljeriya ta gabatarwa gwamnatin sojin Nijar
Wallafawa ranar:
Kunna - 16:12
A daidai lokacin da aka gaza tattaunawa tsakanin sojojin da suka kwaci mulki a Jamhuriya Nijar da kuma kungiyar Ecowas, a nata bangare Aljeriya, ta ce ta samu wasikar amincewa da tayin shiga tsakanin da kasar wadda ke Arewacin Afirka ta gabatar wa gwamnatin sojin.
Kimanin makonni 5 da suka gabata ne Aljeriya ta ce tana goyon bayan kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta share watanni 6 kafin shirya zabuka a Nijar.
Duk da yake ba su ce za su yarda a gudanar da zabe cikin watanni 6 masu zuwa ba, amma sojojin sun amince Aljeriya ta shiga tsakani a wannan takaddama.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Nasiru Sani ya gabatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu