Isa ga babban shafi
Wasanni

Rawar da kasashen Afrika suka taka a wasannin Olympic a birnin Tokyo na Japan

Wallafawa ranar:

Kimanin makwanni biyu kenan da aka kammala wasannin Olympic na Tokyo 2020, inda kasashen duniya 205 da kuma ‘yan wasa fiye da  dubu 11 suka barje gumi a mabanbantan wasanni.

Alamar wasannin  olympics na Japan
Alamar wasannin olympics na Japan NICOLAS ASFOURI AFP/Archives
Talla

Amurka da China da Japan da Birtaniya da Rasha ke kan gaba wajen samun lambobin yabo na zinari da azurfa da kuma Tagulla, yayin da kasashen Afrika aka yi musu fintinkau, in ban da ma Kenya wadda ta fi taka rawar gani a nahiyar Afrika, domin kuwa ta lashe zinari 4 da azurfa hudu da tagulla biyu kuma ita ce ta farko a nahiyar amma ta 19 a duniya.

Wasannin Olympics na Japan
Wasannin Olympics na Japan © AP - Kiichiro Sato

To ko me masana lamurra wasanni za su ce game da rawar da Kasashen Afrika suka taka a gasar?

Olympics na kasar  Japan
Olympics na kasar Japan AP - Jae C. Hong

Wani abun da ake ganin tamkar abin kunya ne shi ne yadda ‘yan wasan Najeriya suka gudanar da zanga-zanga a can birnin na Tokyo saboda wasu dalilai da suka hada da haramta ma wasunsu fafatawa saboda ta’amulli da kwayoyi kamar yadda gwaji ya nuna, yayin da kamfanin Puma ya soke yarjejeniyar Dala miliyan 2.7 da ke tsakaninsa da Najeriya saboda abubuwan da suka wakana a Tokyon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.