Isa ga babban shafi
Siyasa

Sharhi Kan Jam’iyyar ACN Da ‘Yan Takararta

Wallafawa ranar:

Jam’iyyar ACN jam’iyya ce wacce ta mamaye yankin kudu maso yammacin Najeriya, Jam ‘iyyar ce ta lashe kujerun gwamnoni hudu a yankin da suka hada da jahar lagos, Ekiti, Edo da kuma Osun. Sai dai jam’iyyar bata da wakilci a sauran yankunan kasar Musamman ma yankin Arewaci.A zaben da ya gabata na 2007 a kasar, Jam’iyyar ta shiga takara ne da sunan AC inda ta tsayar da Tsohon mataimakin shugaban kasa Alh. Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa wanda ya kara da tsohon shugaban kasa marigayi Ummaru Musa Yar’adua. Bayan da Jam’iyyar ta shiga kawance da wasu Jam’iyyun adawa a kasar musamman ma Jam’iyyar DPP ta tsohon Gwamnan Sokoto Alh. Attahiru Bafarawa Jam’iyyar ta canza suna zuwa ACN Domin tunkarar zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Aprilun shekarar 2011. 

Talla

Mallam Nuhu Ribadu wanda ya fito daga jahar Adamawa shiyar arewa maso gabacin Najeriya kuma shi Jam’iyyar ACN ta tsayar a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa. Ribadu shi ne tsohon shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa. Sai dai wasu suna hangen cewa Mallam Nuhu Ribadu wanda Jam’iyyar ta tsayar a 14 ga Fabrairu yana da sabanin ra’ayin siyasa da jigon Jam’iyyar Bola Tinubu da bagoya bayansa.

Ni nafi dacewa in shugabanci Nigeria

A karshen watan Janairu ne Mallam Nuhu Ribadu ya zabi Sunny Ugochukwu dake zaune a kasar Amurka a matsayin mataimakin shugaban kasa wanda zai mara masa baya a zaben watan Aprilu.

Mista Oguchukwu wanda ya fito daga jahar Anambra kuma dan kasuwa dake tafiyar da kasuwancinsa a Dallas Jahar Texas a kasar Amurka, ya taba zama shugaban yakin neman zaben Mallam Nuhu Ribadu.

Mallam Nuhu Ribadu, ya sha alwashin gudanar da shugabanci na gari da rikon gaskiya da amana idan har aka zabe shi tare da kokarin tabbatar da tafiyar gwamnatinsa da ‘yan najeriya mazauna kasashen waje a al’amarin da ya sanya ya dauko Ugochukwu a matsayin mataimakinsa.
KALUBALE
Babban kalubalen da jam’iyyar ACN zata fuskanta yayin zaben wannan shekara ta 2011 da za a gudanar a tarayyar Nigeria, shi ne fadada karfin jam’iyyar zuwa yankuna musamman na arewacin kasar.

Bayan watsewar yunkurin hadakar jam’iyyun adawa, tana kara fitowa fili cewa tilas ko wacce jam’iyya ta tashi tsaye wajen shiga lunguna da sakuna na kasar, tare da neman magoya baya, saboda kalubalen da suke fuskanta na tunkarar jam’iyyar PDP mai mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.