Isa ga babban shafi
Siyasa

Sharhi kan Jam’iyyar ANPP da ‘yan takararta

Wallafawa ranar:

Jam’iyyar ANPP jam’iyya ce wacce ta dade tana adawa da Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar tun zaben shekarar 1999 da sojoji suka mika mulki ga farar hula. Sai dai a lokacin Jam’iyyar ta shiga zabe ne da sunan APP kafin zaben 2003 ta canza suna zuwa jam’iyyar ANPP.A zaben 1999, Jam’iyyar ANPP ta samu mamaya a yankin arewacin kasar inda ta lashe kujerun gwamnoni 9 da suka hada da jahar Borno, Gombe, Jigawa, Kebbi, kwara, Kogi, Sokoto Jahar Yobe da Zamfara. Sai dai kuma a zaben 2003 Jam’iyyar ta rasa kujerun gwamna guda uku. Har zuwa zaben 2007 inda ta kara rasa wasu kujerunta na gwamnan Sokoto da Jigawa kodayake ta samu karin kujerar gwamnan Bauchi wanda daga baya da shi da Gwamnan Zamfara suka canja sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Talla

SHEKARAU YASAKE NUNE A KANO

A yanzu haka dai Jam’iyyar ANPP na da kujerun jahohi gwamnoni Uku ne da suka hada Kano da Borno da kuma jahar Yobe.

A zaben shekarar 2003 da 2007, Gen. Muhammadu Buhari ne jam’iyyar ke tsayarwa a matsayin takararta na shugaban kasa, bayan kammala zaben 2007 ne Jam’iyyar ta shiga gwamnatin hadin gwiwa da Gwamnatin Marigayi Ummaru Musa Yar’Adua wanda aka bayyana ya lashe zaben shugabancin kasar karkashin Tutar Jam’iyyar PDP al’amarin da ya sanya Janar Muhammadu Buhari ya fice daga Jam’iyyar.

Domin tunkarar zaben shugaban kasa a watan Aprilun bana, Jam’iyyar ANPP a yanzu haka Gwamnan Jahar Kano ne Mallam Ibrahim Shekarau ta tsayar a matsayin dantakararta tare da John Odigie Oyegun a matsayin mataimakinsa.

Mallam Ibrahim shekarau wanda ya kwashe shekaru 8 yana shugabancin jahar Kano, masu sharhi kan lamurran siyasa suna ganin babu wata rawar da zai taka a zaben, musamma ma jaharsa ta kano inda Abokin Hamayyarsa Janar Muhammadu Buhari ke da yawan magoya baya. Sai dai kuma Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa idan har ya samu nasarar Lashe zaben shugabancin kasar zai yi kokarin gudanar da shugabancin na adalci wanda zai samar da yadda tsakanin masu mulki da wadanda ake shugabanta.

A tafiyar Shekarau da Odigie masana dai suna ganin Shekarau ya zabi tumun dare, ganin cewa Mista Odogie shi ne tsohon gwamnan jahar Edo da aka zaba karkashin Tutar jam’iyyar SDP zamanin Mulkin tsohon shugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida tsakanin shekarar 1992 zuwa 1993 wanda masu sahrhi suke masa kallon baya da tasiri a siyasar jaharsa da ma kasa baki daya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.