Isa ga babban shafi
Siyasa

Illolin Dage Zabe

Wallafawa ranar:

Binciken masana kimiyyar siyasa ya tabbatar da cewa zabe karkashin mulkin dimokiradiyya,wani al'amari ne dake chin makuden kudade wajen shiri da aiwatarwa. A kan haka galibin hukumomin da ake dorawa nauyin gudanar da zabubbukka,kan kebe ranaku na musamman domin samun saukin gudanar da wannan aikin.Sai dai kuma a duk lokacin da hukumomi zabe suka dage ranar gudanar dashi,bangarorin dake da dangantaka da zabe kan samu kansu cikin wani mawuyacin hali. Kama daga ita kanta hukumar zabe ya zuwa 'yan takara mukamai dama masu kada kuria,kowa zai ji a jikin sa.Shirin Duniyar Mu A Yau na wannan makon,ya duba wasu daga cikin matsaloli ko kuma illolin dake bayyana,daga dage zaben da aka sa ranar gudanar dashi. A nan shirin yayi misali da kashin farko na zabubbukkan Nigeria wanda aka dage har sau biyu bisa wasu dalilai.

RFI Hausa
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.