Isa ga babban shafi

Amurka: Ana zargin Trump da yunkurin juyin mulki

Kwamitin da ke binciken harin da wasu ‘yan daba suka kai a majalisar dokokin Amurka a shekarar ta 2021, ya zargi Donald Trump da yunkurin juyin mulki a sanadiyar abin da ‘yan daban suka yi. 

Magoya bayan Trump suna tarzoma a Capitol
Magoya bayan Trump suna tarzoma a Capitol AP - Manuel Balce Ceneta
Talla

A sakamakon binciken farko da aka yi na tsawon shekara guda, kwamitin na musamman ya yi kokarin nemo mafita kan kokarin da tsohon shugaban kasar  Trump ya yi na kawo rudani a sakamon zaben kasar na shekarar 2020 da Joe Biden ya lashe.

Lokuta kadan kafin hakan, shugaban kwamitin dan jam'iyyar Democrat Bennie Thompson, ya zargi Trump da kulla wannan makarkashiyar.

Kwamitin ya yi amfani da shaidu da wasu manya da amintattun Trump suka bayar, ciki har da tsohon babban lauyan gwamnati Bill Barr da kuma babban hadiminsa Jared Kushner.

Zaman  na ranar Alhamis da ta gabata, da kuma sauran biyar da za a yi a makonni masu zuwa za a mayar da hankali ne kan rawar da Trump ya taka a kokarin ci gaba da zama a matsayinsa ta hanyar tauye kuri’un miliyoyin mutane.

Bayan sauraron rahoton, Trump ya sake yin kakkausar suka game da zargin da ake yi masa, inda ya zargi kwamitin da nuna son kai.

Jami’ar ‘yan sandan Capitol, Caroline Edwards, wacce ta kasance a wajen da aka balle katangar farko, ta bayyana irin raunin da ta samu a arangamar da suka yi da ‘yan kungiyar da suka tayar da tarzomar.

Kwamitin dai bai bayyana matakin da yake  shirin dauka na gaba ba,  bayan kammala zaman sauraren rahoton, amma ana sa ran za a sake gabatar da wani rahoto na karshe a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.