Isa ga babban shafi

Ana tsare da Shugaban yan adawa da wasu magoya bayan sa a Equatorial Guinea

Hukumomin kasar Equatorial Guinea sun kama wani shugaban 'yan adawar kasar Gabriel Nse Obiang Obono tare da magoya bayansa 150 lokacin da Yan Sanda suka kai samame a gidan sa.

Gabriel NSE obiang Obono,Jagoran yan adawa na Equatorial GUINEA
Gabriel NSE obiang Obono,Jagoran yan adawa na Equatorial GUINEA © AP
Talla

Wannan na zuwa ne mako guda bayan da shugaban kasa Teodoro Obiang Nguema ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar zabe domin yin wa’adi na 6, bayan ya kwashe shekaru 43 a karagar mulki.

 Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang, a 2019 a Paris
Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang, a 2019 a Paris AFP - LUDOVIC MARIN

Sanarwar gwamnatin kasar tace an kama Obono ne jiya alhamis a gidansa bayan yaki amsa gayyatar da aka masa daga bangaren mai gabatar da kara.

Rahotanni sun ce lokacin da ake kokarin daukar sa daga gidansa, magoya bayan sa sun yi harbi inda suka kashe dan sanda guda.

Shugaban kasar tare da wasu daga cikin magoya bayan sa lokutan sanar da sakamakon zaben shekarar 2016
Shugaban kasar tare da wasu daga cikin magoya bayan sa lokutan sanar da sakamakon zaben shekarar 2016 STR / AFP

Obono yayi barazanar kaddamar da zanga zanga a kwanaki masu zuwa domin nuna bacin ransa akan yadda gwamnati ta haramta masa shiga zaben shugaban kasa da na Yan majalisun da za’ayi ranar 20 ga watan Nuwamba.

Hukumar zabe ta soke Jam’iyyar Obono ta CI bayan lashe kujera guda na majalisa daga cikin kujeru 100 a zaben da akayi a shekarar 2017.

Jam’iyyar shugaban kasa Obiang ta PDGE ce ta lashe sauran kujeru 99 dake Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.