Isa ga babban shafi

Chadi ta sanar da tsawaita wa’adin mika mulki ga fararen hula

Kasar Chadi ta sanar da tsawaita wa’adin mika mulki ga fararen hula da akulla na Karin shekaru biyu a daidai lokacin da ake shirin kamala taron kasa gobe Asabar, tare da baiwa  Mahamat Idriss Deby Itno  damar ci gaba da rike mukamin shugaban gwamnatin mulkin soji da kuma ba shi damar tsayawa takarar shugabancin kasar.

Taron sassanta yan kasar Chadi
Taron sassanta yan kasar Chadi AFP - AURELIE BAZZARA-KIBANGULA
Talla

Daruruwan wakilan da suka halarci taron sasanta rikicin siyasar kasar wanda yan adawa da  kungiyoyin farar hula da yan adawa ne suka kauracewa ne suka goyi bayan shirin.

An kaddamar da wannan tattaunawar ta kasa ce a ranar 20 ga watan Agusta, watanni 16 bayan da matashin shugaban Janar Mahamat Idriss Deby Itno, mai shekaru 37, ya  hau karagar shugabanci Chadi, washegarin rasuwar mahaifinsa, Idriss Deby Itno, wanda aka kashe a fagen daga a ranar 21 ga Afrilu, 2021.

Shugaban Majalisar sojin kasar Chadi Mahamat Déby a lokacin soma taron sassanta yan kasar a Djamena
Shugaban Majalisar sojin kasar Chadi Mahamat Déby a lokacin soma taron sassanta yan kasar a Djamena AFP - AURELIE BAZZARA-KIBANGULA

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bayyana damuwarta a ranar Lahadin da ta gabata game da matakin da aka dauka a kasar Chadi na tsawaita wa'adin mika mulki da bai wa shugaban gwamnatin mulkin soja Mahamat Deby Itno damar tsayawa takarar shugabancin kasar.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Turai ta fitar, ta bayyana damuwarta game da wasu shawarwarin da aka cimma, dangane da tsarin zabukan dake tafe, ta yadda ba za su yi la'akari da sanarwar kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika  ba, dangane da tsawon lokacin mika mulki da kuma batun rashin cancanta da ya shafi hukumomin da ke aiwatar da shi.

Kungiyar kasashen Turai da ofisoshin jakadancin Faransa, Jamus, Spain da Netherlands a Chadi ne suka bayyana wannan damuwa,kazzalika yan adawa da wasu kungiyoyin farraren hula da yan tawaye sun janye daga zaman taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.