Isa ga babban shafi

Shugaban Equatorial Guinea ya kaddamar da takarar neman wa'adi na shida

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin kasarsa da karfen kafa, ya kaddamar da takararsa na neman wa'adi na shida a yakin neman zabe na farko.

Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea  kenan
Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea kenan REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Obiang mai shekaru 80 a duniya ya hau karagar mulki ne a shekara ta 1979 kuma shi ne shugaban kasa mafi dadewa akan karagar mulki a duniya ban da sarakuna. Ba a taba sake zabensa a hukumance da kasa da kashi 93 na kuri’un da aka kada ba.

Jam'iyyarsa mai rinjaye ta DPEG ta fara yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da na kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 20 ga watan Nuwamba a garin Ebebiyin da ke arewacin kasar kusa da kan iyaka da Kamaru.

Obiang ya shaidawa daruruwan magoya bayansa cewa jam'iyyarsa ta zabe shi ya tsaya takara saboda shi ne alamar zaman lafiya da ke mulki a Equatorial Guinea.

Bayanin zabensa ya ta'allaka ne kan ci gaba da bunkasa kasar da ke Tsakiyar Afirka, mai dimbin albarkatun man fetur da iskar gas amma galibin al'ummar kasar na rayuwa cikin talauci.

Jam’iyyar PDGE dai na da kujeru 99 daga cikin 100 na majalisar wakilai da kuma dukkanin kujerun a majalisar dattawa.

Wadanda za su fafata da Obiang sun hada da Andres Esono Ondo na jam’iyyar Convergence for Social Democracy da Buenaventura Monsuy Asumu, mai wakiltar jam’iyyar Democratic Social Coalition.

Fiye da masu kada kuri'a 425,000 ne suka yi rijistar zabe daga cikin al'ummar kasar kusan miliyan 1.4.

Equatorial Guinea dai na daya daga cikin kasashen duniya masu karfin iko kuma ta rufe kan iyakokinta da Kamaru da Gabon a farkon wannan mako, tana mai cewa tana son hana kungiyoyi kutsa kai a harkokin zabenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.