Isa ga babban shafi

Amurka ta ce ta damu da zaben Najeriya

Kasar Amurka ta bukaci ganin an gudanar da karbabben zabe mai inganci a Najeriya, yayin da take cewa kasar na da matukar muhimmanci ga duniya baki daya. 

Shugaban Amurka Joe Biden kenan
Shugaban Amurka Joe Biden kenan REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

Wani sako na musamman da manyan jami’an gwamnatin ta suka nada ta bidiyo mai tsawon mintina 58 suka aikewa jama’ar kasar, ya janyo hankalin ‘yan siyasa da kuma jama’a baki daya da su bada gudumawa wajen ganin anyi zabe mai inganci a karshen wannan mako. 

Cikin wadanda suka gabatar da sakonninsu a bidiyon sun hada da Sakataren harkokin waje Anthony Blinken da Babbar jami’ar USAID Samantha Power da Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield. 

Sakon ya bayyana cewar ‘yan Najeriya sun sake samun wata dama na bayyana ra’ayoyinsu da kuma zabin shugaban da suke bukata ta hanyar zabe saboda muhimmancin kuri’un su. 

Blinken yace muhimmancin wannan zaben da zai gudana a karshen wannan mako ba wai ya tsaya kawai ga Najeriya bane, har ma da duniya baki daya. 

Wakilan gwamnatin sun jaddada cewar Amurka bata goyan bayan wani ‘dan takara guda, amma kuma tana goyan bayan shirin wanda zai baiwa jama’ar kasar zabin abinda suke so ta hanyar lumana. 

Sakon yace samun gudanar da karbabben zaben cikin kwanciyar hankali zai taimaka wajen samun dorewar zaman lafiya a duniya baki daya. 

Ko a jiya Talata, tsohon shugaban kasar Brack Obama ya gabatar da irin wannan sako ga ‘yan Najeriya inda ya bukace su da su taimaka wajen ganin an gudanar da ingantaccen zabe cikin kwanciyar hankali. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.