Isa ga babban shafi

Majalisar tsaron Najeriya tace babu abinda zai hana zabe ranar asabar

Majalisar tsaron Najeriya tace babu abinda zai hana gudanar da zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisun tarayya a ranar asabar mai zuwa kamar yadda aka tsara, duk da ‘yan matsalolin da ake fuskanta nan da can. 

Shugaban hukumar zaben Najeriya  Mahmood Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmood Yakubu. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ministan shari’a Abubakar Malami ya shaidawa manema labarai haka bayan wani taron da majalisar ta gudanar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, tare da karbar bayanai daga Hafsan Hafsoshin sojin kasar Janar Lucky Irabor da shugabannin rundunonin sojin sama da kasa da ruwa tare da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Baba Alkali. 

Malami yace bayan gamsuwa da bayanan da shugabannin hukumomin tsaron suka gabatar, majalisar ta bada umurnin ci gaba da shirin zaben kamar yadda aka shirya a ranar 25 ga wata, kamar yadda majalisar zartarwa da majalisar bada shawara ta tsoffin shugabannin kasa suka bada umurnin. 

Ita ma Hukumar zaben kasar tace ta shirya tsaf domin ganin an gudanar da zaben kamar yadda doka ta tanada, wanda za’a fara da zaben shugaban kasa da majalisun tarayya, kana a biyo da na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan gobe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.