Isa ga babban shafi

An kama dan Majalisar PDP da dala 500,000 a Fatakwal

‘Yan sanda sun cafke dan majalisar tarayya mai wakiltar Fatakwal ta II, Chinyere Igwe, bayan samun sa da takardun kudi na dalar Amurka kusan 500,000, gabanin zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

Chinyere Igwe
Chinyere Igwe © dailytrust
Talla

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, ta tabbatar da cewa an cafke dan majalisar da makudan kudin ne, yayin da yake neman sake darewa a kurarar da yake kai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin SP Grace Iringe Koko, ta ce dan majalisar karkashin inuwar jam’iyyar PDP, an kuma same shi da takarda mai kunshe da sunayen wadanda za a rabawa kudin.

Wannan na zuwa ne, yayin da hukumar zaben kasar ke cigaba da jan hankulan jami’anta game da karbar kudade a hannun ‘yan siyasa, inda kungiyoyin fararen hula ke ci gaba da wayar da kan jama’a kan yadda zza su kaucewa sayar da kuri’insu.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wata kotun Majistare da ke zama a Fatakwal ta tura dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Etche/Omuma a majalisar wakilai ta tarayya, Honarabul Ephraim Nwuzi zuwa gidan gyaran hali.

Rundunar ‘yan sandan ta zargi dan majalisar tarayya, wanda kuma dan takarar jam’iyyar APC ne a zaben ranar 25 ga Fabrairu, 2023 da laifin cin amanar kasa, hada baki, yunkurin hada rikicin kabilanci da sauran su.

Siyan kuri’u ya kasance babban kalubale a zaben Najeriya, inda hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun sha alwashin murkushe ‘yan siyasar da ke neman sayen masu kada kuri’a a zaben 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.