Isa ga babban shafi

Zabe Najeriya: Buhari ya bayar da umarnin a rufe iyakokin kasar

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin rufe dukkanin iyakokin kasar, yayin da ake shirin gudanar da babban zaben kasar mai cike da takaddama a ranar Asabar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron kasashen Afirka da Amurke da ke gudana a Washinghton DC na kasar Amurka . 14/12/22
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron kasashen Afirka da Amurke da ke gudana a Washinghton DC na kasar Amurka . 14/12/22 © Bashir Ahmad
Talla

Umurnin na da nufin tabbatar da cewa “zabukan sun kasance cikin ‘yanci, adalci kuma ba tare da wata matsala ba”, in ji Hukumar Shige da Fice ta Najeriya.

Hukumar ta ce, tuni ta umarci jami’anta na kan iyaka da su tabbatar da aiwatar da doka da oda.

Rahotanni sun ce zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki sun kasance masu cike da sarkakiya, tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.

Hukumar kula da shige da fice ta kasar ta ce ta kwace katunan zabe 6,000 da wasu takardu na tantance ‘yan Najeriya daga hannun ‘yan ci-rani.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci hukumomin tsaro da su kasance masu jajircewa a lokacin zabe, sannan ya yi gargadin kaucewa tayar da tarzoma bayan bayyana sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.