Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya: Ana ci gaba da bankado masu sayen kuri'u

Kusan mutane miliyan 90 ne ake sa ran za su kada kuri’a a ranar Asabar, domin zabar wanda zai gaji shugaban kasar Muhammadu Buhari da zai sauka daga mulki bayan wa’adi biyu, sai dai kuma ana ganin zai bar kasar cikin mawuyacin hali na matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.

Wata mata yayin kada kuri'ar yayin zaben shugaban kasa a birnin Lagos dake Kudancin Najeriya. 14/04/2007.
Wata mata yayin kada kuri'ar yayin zaben shugaban kasa a birnin Lagos dake Kudancin Najeriya. 14/04/2007. AP - SUNDAY ALAMBA
Talla

Ana sa ran za a gudanar da zabukan tsakanin ‘yan takara hudu: Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, da dan takarar babbar jam’iyyar adawa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, sai Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.

A jihar Ribas mai arzikin man fetur, ‘yan sanda sun kama wani dan majalisa dauke da buhun kudi da ake zargin yana sayen kuri’u.

Jami’an ‘yan sanda daga jihar Ribas sun kama Honourable Chinyere Igwe, dan majalisar wakilai (daga jam’iyyar PDP) da kudi dalar Amurka 498,100 a cikin jaka,” in ji kakakin ‘yan sandan, Grace Iringe-Koko.

Haka kuma an gano jerin sunayen wadanda za a raba wa kudaden.

A wani labarin kuma, hukumomi a jihar Legas sun gano kwatankwacin dala 70,300 da aka boye a cikin takardun kudin kasar wato Naira wanda kuma ake zargin za a yi amfani da shi wajen siyan kuri’u.

Haka zalika, jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun kama Naira miliyan 32,400,000, inji hukumar a shafinta na Facebook.

Sanarwar ta kara da cewa, an tsare wanda ake zargi da hannu domin ci gaba da yi masa tambayoyi, ba tare da bayar da karin bayani ba.

Zabubbukan Najeriya sau da yawa ana yin sa ne ta hanyar sayen kuri'u.

A wani yunkuri na shawo kan lamarin, babban bankin ya fitar da sabbin takardun kudi na Naira a watan Disamba, inda ya baiwa ‘yan Najeriya wasu makwanni kadan su maye gurbin tsofaffin.

Musayar kudin dai ya sa 'yan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali, 'yan kwanaki kadan a gudanar da zabe mai mahimmanci a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.