Isa ga babban shafi

Ya kamata INEC ta soke zaben shugaban kasa a wasu yankuna - Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce ya kamata a soke zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar a wasu yankunan, sakamakon cewa yana cike da kurakurai.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yayin halartar taron tattalin arzikin duniya kan Afirka a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Mayu 11, 2012.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, yayin halartar taron tattalin arzikin duniya kan Afirka a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Mayu 11, 2012. © REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Tsohon shugaban kuma bukaci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu da ya ceci Najeriya daga cikin hadari da bala’i da ke neman faruwa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken "Zaben Shugaban Kasa na Najeriya na 2023: Ana bukatar gyara da kuma daukar matakn gaggawa."

A cewarsa, ba wani boyayyen abu ba ne cewa jami’an hukumar ta INEC a matakin aiki ana zargin an yi musu katsalandan ne biyo bayan mika sakamakon da hannunsu, da kuma zargin an yi amfani da su wajen yin magudin zabe.

A ranar 1 ga watan Janairu, Obasanjo ya fito fili ya amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, a matsayin wanda ya fi so a zaben watan Fabrairu.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wani sako na sabuwar shekara mai taken " kirana ga daukacin 'yan Najeriya musamman matasan Najeriya."

Tsohon shugaban kasar ya lura cewa babu daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa waliyyi, amma idan aka kwatanta da ilimi, da’a da kuma abin da za su iya bayarwa, Peter Obi ya cancanta ya shugabanci Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.