Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya: Guguwar canji ta tafi da kujerun sanatoci da dama

Yayin da ake ci gaba da gabatar da sakamakon zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun Najeriya da akayi a karshen mako, bisa dukkan alamu an samu guguwar da ta raba wasu ‘yan majalsiun da kujerunsu, abinda ke nuna cewar ba zasu samu damar komawa majalisar ba. 

Yadda masu kada kuri'a ke gudanar da zabe a Najeriya
Yadda masu kada kuri'a ke gudanar da zabe a Najeriya © dailytrust
Talla

Daga cikin irin wadannan ‘yan majalisu akwai Sanata Kabir Ibrahim Gaya na Jam’iyyar APC a Jihar Kano wanda ya sha kaye a hannu tsohon ‘dan majalisar tarayya Hon Kawu Sumaila, sai kuma Sanata Ahmad Babba Kaita daga Jihar Katsina wanda ya sha kaye a hannun Nasir Sani Zango. 

Mai magana da yawun majalisar dattawa, Sanata Ajibola Ashiru na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun Olubiyi Fadeyi na Jam’iyyar PDP a Jihar Osun, sai kuma Sanata Biodun Olujimi na Jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti ya sha kaye a hannun ‘dan majalisar tarayya Yemi Adaramodu na Jam’iyyar APC. 

A jihar Gombe, tsohon gwamna Ibrahim Dankwambo ya kada Sanata Saidu Alkali na Jam’iyyar APC, kuma wanda ya rike da kujerar Gombe ta arewa, yayin da Sanata Danjuma Goje ya sake lashe kujerarsa, sai kuma Sanata Anthony Siako Yaro da ya lashe kujerar Gombe ta kudu bayan kada sanata Joshua Lidani. 

Sai kuma gwamnonin Cross Rivers da Enugu da kuma Benue da suka rasa damar zuwa majalisar dattawa saboda shan kayen da suka sha a hannun abokan karawarsu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.