Isa ga babban shafi
Afrika - Tattalin Arziki

Adalci a rabon rigakafin Korona zai gaggauta farfado da arzikin Afrika - WTO

Shugabar hukumar kasuwanci ta duniya WTO dakta Ngozi Okonjo Iweala ta ce Afrika na matukar bukatar daidaito tsakaninta da kasashe masu arzikin wajen rabon alluran rigakafin cutar Korona, domin gaggauta farfado da tattalin arzikin kasashen nahiyar.

Shugabar hukumar kasuwanci ta duniya WTO dakta Ngozi Okonjo Iweala.
Shugabar hukumar kasuwanci ta duniya WTO dakta Ngozi Okonjo Iweala. SALVATORE DI NOLFI POOL/AFP
Talla

Tsohuwar ministar kudin Najeriyar ta bayyana haka ne yayin gabatar da jawabi a wurin wani taron kwararru kan tattalin arziki da bankin UBA ya shirya a Najeriyar.

Ngozi Okonjo Iweala ta kuma bayyana fatan samun nasarar shirin asusun IMF na ware dala biliyan 50 domin yiwa kashi 40 na yawan al’ummar duniya allurar rigakafin Korona zuwa karshen wannan shekara, yayin da kuma za a yiwa ragowar 60 a shekarar 2022.

A cewar shugabar hukumar kasuwancin ta duniya, muddin shirin na IMF ya samu nasara, karfin tattalin arzikin duniya zai karu da akalla dala tiriliyan 9 nan da shekarar 2025.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.