Macron ya bukaci kasashe masu arziki su taimakawa Afrika da allurar rigakafin korona
Shugaban Fransa Emanuel Macron, ya shawarci kasashen masu karfin arziki da su ware kashi 3 zuwa 5 na magungunan rigakafin da su ka mallaka dan tallafawa kasashen Afrika.
Wallafawa ranar:
Wannan kira, na Shugaba Macron dai baya rasa nasaba da laakari da fadi tashin da kasashen Afrika ke yi dan ganin sun samar da maganin rigafin wa alummarsu, lamarin da yazo kwana guda kafin taron gungun kasashe 7 masu karfin arziki na duniya, a kasar Birtaniya. Ya kara da cewa, gazawa wajen aiwatar da hakan, hakika ba zai haifar da d’a mai ido ba, wa kasashen duniya.
Macron, yace Waziyariyar kasar Jamus Angela Merkel na goyon bayan kungiyar kasashen turai kuma yana fatan za’a shawo kan Amurka ma.
Sai dai kuma zuwa yanzu wasu kasashe matalauta na cikin duhu a kan cutar, a ya yin da kasashen da suka ci gaba masu karfin arziki,tuni su ka fara allurer rigakafin cutar,a cewar sa,lamarin da yace ba za’ a amince dashi ba domin hatsarinsa wa duniya.
Macron, dan shekaru 43 ya amince da tsarin China na rabawa kasashe mabukata maganin allurar rikafin da sukewa kallon kaskantar da kai ne yayin da wasu ke saya kamar Pakistan da Turkey da Hadediyar Daular Larabawa da wasu daga nahiyar Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu