Isa ga babban shafi
OPEC - Tattalin Arziki

OPEC ta amince da kara yawan man da manbobinta ke hakowa daga watan Agusta

Kasashe masu arzikin man fetur na ciki da wajen kungiyar OPEC sun cimma matsayar amincewa da shirin kara yawan gangunan danyen man fetur da suke hakowa sannu a hankali daga watan Agusta mai zuwa.

Tambarin kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur.
Tambarin kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur. © Reuters
Talla

Taron kasashen na ciki da wajen OPEC ya amince da karin gangar danyen mai dubu 400 kan adadin fiye da miliyan 3 da suke fitarwa a kowace rana daga Agusta don taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya yayin da cutar Korona tayi sauki a wasu sassa.

Kasashen na OPEC da kawayensu sun amince da wannan mataki ne a yau Lahadi bayan da a farkon watan Yulin da muke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakile yunkurina kulla yarjejeniyar, sakamakon takaddamar da ta kaure tsakaninta da Saudiya.

Manufar kasashen masu arzikin mai dai ita ce komawa kan matakin fitar gangar danyen man miliyan 5 da dubu 800 a kowace rana, kamar yadda suke yi kafin barkewar annobar Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.