Girka
Majalisar Girka ta amince da harajin gidaje
Majalisar Kasar Girka, ta amince da shirin karbar harajin gidaje, matakin da ya samu mummunar suka daga al’ummar kasar, wadanda suka shiga zanga zanga, don nuna adawa da shirin.Wannan mataki yana daga cikin Sharuddan da kungiyar kasahsen Turai ta tsara, kafin sake tallafawa kasar Girka.Ministan kudin Girka, Evangelos Venizelos, yace abinda ke gaban su, shine cim ma muradin kasafin kudin bana da badi.
Wallafawa ranar: