FARANSA
Socialist zata sake gudanar da zaben fitar da gwani
Jam’iyyar Gurguzu ta Socialists a kasar Faransa, zata sake gudanar da zaben tsayar da ‘Yan takara, zagaye na biyu a karshen wanna makon, sakamakon rashin samun gwani a zaben da aka yi.Francois Hollande, wanda ya samu kashi 39, zai kara ne da Martine Aubry, da ta samu kashi 31, don tsayar da wanda zai kalubalanci shugaba Nicolas Sarkozy a zabe mai zuwa.
Wallafawa ranar: