Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa zata rage kudin harajin kamfanoni masu jari mai kauri

A kokarin da take yi na ganin cewa ta dauki matakan kare tabarbarewar arzikinta, kasar Faransa ta ce zata rage kudaden harajin kamfanonin da kan juya kudade, da yawansu ya kai biliyan 20 na kudin Euro. Firaminstan Jean Marc Ayrault, ne ya bayyana cewa kasar ta Faransa, za ta dauki matakan, wandanda suka hada da rage tsadar yin kasuwanci a kasar da kuma rage kudaden da ake kashewa domin habaka harkar kasuwanci. 

Firaministan Faransa, Jean Marc Ayrault
Firaministan Faransa, Jean Marc Ayrault REUTERS/Charles Platiau
Talla

A cewar Ayrault, lokaci ya yi da kasar ta Faransa za ta koma gurbinta, a cikin hadahadar kasuwancin duniya, inda ya kara da cewa, hakan ya sa gwamnatin ta dauki alwashin aiwatar da dukkanin shawarwarin da rahotan hamshakin dan kasuwannan, Louis Gallois, ya bayar.

Wadannan matakai da Faransa zata dauka dai, sun biyo bayan wani kashedi ne da Hukumar bada lamuni ta, IMF ta yi wa kasar Faransan, inda ta gargade ta da cewa, idan bata yi a hankali ba, zata fada cikin halin kakani kayin da makwabtanta na kasashen Spain da Italiya suka shiga.

A dai cewar Ayrault, Faransa bata fada cikin wannan halin ba, sai dai yana da matukar muhimmanci a aiwatar da wadannan shawarwari domin kasar ta tafi kafada da kafada da sauran kashen duniya ta fuskar kasuwanci.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.