Netanyahu yana ziyara Faransa domin karrama yahudawan da aka kashe a Toulouse
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu tare da shugaban Faransa Francois Hollande. zai halarci bikin tunawa da wasu dalibai uku yahudawan Isra’ila da wani Dan bindiga, Mohammed Meira ya harbe a makarantar Yahudawa a watan Maris.
Wallafawa ranar:
Bayan shugabanin biyu sun kwashe lokaci a jiya Laraba suna tattaunawa kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da kuma Iran, shugabanin za su ziyarci makarantar yaran a garin Tolouse a ranar Alhamis.
Wannan ita ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Francois Holland da Benjamin Netanyahu tun bayan karbar ragamar tafi da kasar a watan Mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu