Isa ga babban shafi
EU

Kasashen Turai sun cim ma yarjejeniyar ba Babban Bankinsu karfin kula da bankunansu

Ministocin kasashen Turai sun cim ma yarjejeniyar ba Babban Bankinsu karfin kula da bankunansu wanda zai sa ido ga ayyukan bankunan na bai daya, mai karfin fada aji a Yankinsu kafin su gudanar da babban taronsu a Brussels.

Tambarin kungiyar kasashen Turai masu amfani da kudin Euro
Tambarin kungiyar kasashen Turai masu amfani da kudin Euro REUTERS/Alex Domanski
Talla

Bayan kwashe sa’oi 14 ana tafka mahawara ministocin sun amince da shirin, wanda shugabanin za su amince da shi a ganawar da za su yi a Brussels

A bangare daya kuma ministan kudin Faransa yace Girka ta cika sharuddan kara mata wani sabon tallafi.

Tuni dai kungiyar kasashen Turai ta EU ta amince da bukatar Babban Bankin Nahiyar ECB ya kasance babban mai sag a harakokin bankunan kasashen Nahiyar.

A tsarin yarjejeniyar, kasashe masu yawan kudin da suka kai sama da Euro Biliyan Talatin za su kasance karkashin kulawar Babban Bankin Nahiyar Turai.

Sai dai kuma duk da wannan Birtaniya ta bayyana fargaba game da ci gaban sabon tsarin da kasashen suka amince da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.