Ruftawar gini ya kashe mutane biyu a Italiya
Wani gini daya rufta a yankin Sicilia dake kasar Italiya, ya kashe mutane biyu a jiya da daddare. Tun a ranar litinin ‘Yan kwanakwana suka fara sa mutane su kauracewa yankin bayan mazauna yankin sun ce suna jin alamar zubewar gini.
Wallafawa ranar:
Wadanda suka mutu sun hada da Ignazio Accardi, dan shekaru 85 da Antonino Cina, dan shekaru 54, wadanda duk aka cirosu daga kasan ginin.
Rahotannin sun nuna cewa ana neman wasu mata biyu da ba gansu ba, wadanda aka ce shekaransu ya kai 80 da 74.
Har ila yau dunbin mutane sun samu raunuka a lokacin da ginin ya zube, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu