Isa ga babban shafi
Cyprus

Kasar Cyprus ta gindaya sharuddan amfani da Kudi a kasar

Daga cikin sharuddan da Babban Bankin ya gindaya sun hada da hana fitar da Kudade zuwa kasashen waje, da kayyade yawan kudin da matafiya ka iya dauka zuwa waje, da kuma tsananta yin ciniki da Katin kudi ta Credit Card kazalika da rufe biyan masu Takardar fidda Kudi wato Cheque

Babban Bankin kasar Cyprus
Babban Bankin kasar Cyprus AFP PHOTO / LOUISA GOULIAMAKI
Talla

A karkashin wannan Dokar da aka fitar, an haramtawa mutum daukar tsabar kudi da suka zarta Euro 3000, haka kuma an wajabtawa Kamfunna alhakin samar da cikakkun Takardun dake nuni kan kudin da aka shigo da su a kasar da suka zarta Euro 500.

Wannan matsalar tattalin arzikin kasar Cyprus dai ta kai ga bayyanawa masu Asusun ajiyar kudade a Bankuna ga sanin cewar zasu huskanci hasarar akalla kashi 40 cikin 100 na kudaden da suke ajiya a Bankuna da suka zarta Euro 100,000.

‘Yan kasar Cyprus da dama na zargin kasar tasu da cewar bata yi masu adalci ba, idan aka yi la’akari da sauran kasashe masu amfani da kudin Euro da suka cimma karshen matsalar tattalin arzikin su da suka hada da Spain da Girka.

Yanzu haka dai kasar Burtaniya ta bayyana cewar ba zata kara biyan kudin Pensho a Bankunan kasar Cyprus ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.