Shugaban babban bankin Cyprus Andreas Artemis ya ajiye mukaminsa
Shugaban babban bankin kasar Cyprus, Andreas Artemis ya ajiye mukaminsa a dai dai lokacin da kasar ke yunkurin neman tallafi daga kasashen duniya domin ceto tattalin azrikin kasar da ya shiga wani hali. Kamfanin Dallancin labarai na kasar ta Cyprus, ya bayyana cewa za a aika da takardar ajiye aikin nasa gaban gaban kwamitin bankin nan ba da jimawa ba.
Wallafawa ranar:
A jiya Litinin ne kasar Cyprus ta kulla yarjejeniya da Kungiyar Tarayyar Turai inda za a tallafawa kasar da kudin Euro biliyan 10.
Bayanai na nuna cewa Artemis ya kuma ajiye mukamin nasa ne saboda sharuddan da aka gindaya na karbar bashin ceto babban bankin kasar.
Dukkanin bankunan Cyprus dai sun kasance a rufe tun bayan kulla wannan yarjejeniya, inda ake sa ran za su kwashe kwanaki 11 kamin su bude.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu