EU
Kungiyar Turai ta karfafa dokar ayyukan Bankunanta
Majalisar Kasashen Turai ta amince da sabuwar dokar aiyukan bankuna da kuma kudaden garabasar da ake bai wa jami’an bankuna. Dokar ta kunshi amincewa da kashi 100 na albashin ma’aikaci, a matsayin kudin garabasar ko kuma kashi 200 idan masu jari a bankin sun amince da haka. Ana saran fara aiki da sabuwar dokar ranar 1 ga watan Janairun badi
Wallafawa ranar: