Isa ga babban shafi
Cyprus

Shugaban Cyprus ya ce za a hukunta masu hannu a cutar da tattalin arzikin kasar

Shugaban kasar Cyprus Nicos Anastasiades, a yau litinin ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da bincike irin na mai kan uwa da wani domin gano wadanda suka taka rawar da ta kai ga durkusar da tattalin kasar.

Masu zanga-zanga a Cyprus
Masu zanga-zanga a Cyprus Reuters
Talla

Kafafen yada labaran kasar sun bayyana cewa a cikin kwanakin baya-bayan nan wasu na hannun damar shugaban kasar har ma da iyalansa, sun rika kwashe makuddan kudade daga wannan banki zuwa wancan, lamarin da ake kallo a matsayin kafar angulu ga tattalin arzikin kasar da ya jima yana fama da matsaloli.
A cikin makon da ya gabata ne dai gwamnatin kasar ta kafa wani kwamitin bincike mai kunshe da tsoffin alkalan Kotun Kolin kasar uku, wanda aka dorawa a alhakin gudanar da bincike domin gano duk wanda ke da hannu a durkusar da tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.