Isa ga babban shafi
Cyprus

Shugaban Orthodox ya soki shirin tsuke bakin aljihun gwamnatin Cyprus

Shugaban kiristoci mabiya darikar Orthodox a kasar Cyprus Archbishop Chrysos-tomos na biyu a yau lahadi ya yi kira ga ministan kudi da kuma shugaban babban bankin kasar da su sauka daga kan mukamansa, saboda irin rawar da suka taka har kasar ta amincewe ta karbi umurnin Kungiyar Tarayyar Turai domin samun tallafi da kuma tsuke bakin aljihun gwamnatin, abubuwan da shugaban kiristocin ya ce babban bala’i ne ga manyan bankunan kasar.

Babban Bankin kasar Cyprus
Babban Bankin kasar Cyprus REUTERS/Bogdan Cristel
Talla

Archibishop Chrysos-tomos na biyu, ya ce sam bai gamsu ba da irin matakan da mutanen biyu tare da hadin bakin Kungiyar tarayyar Turai suka dauka domin ceto tattalin arzikin kasar, inda ya bayyana su da cewa matakai ne maras amfani da za su kara cutar da tattalin arzikin kasar.
Shugaban na ‘yan Orthodox ya ce ‘’za mu ci gaba da yi wa gwamnatin kasarmu, da babban bankin kungiyar tarayyar Turai da kuma asusun lamuni na duniya matsin lamba domin su fahinci cewa ba ma goyon wadannan matakai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.