Isa ga babban shafi
Cyprus

Masu ajiya a Banki sun samu sassauci a Cyprus

Al’ummar kasar Cyprus suna fatar ci gaba da samun sassauci bayan hukumomin kasar sun takaita sharuddan da suka gindaya wa masu ajiya a bankuna. Wannan nan na zuwa ne bayan shugaban kasar yace tallafin da suka samu daga kungiyar Tarayyar Turai da Asusun bada lamuni na IMF na Euro Biliyan 10 shi ne ya ceto tattallin arzikin kasar.

Harabar bankin Cyprus
Harabar bankin Cyprus REUTERS/John Kolesidis
Talla

Sai dai kuma masu lura da matsalar tattalin arizikin Cyprus sun ce akwai yiyuwar masu ajiya a bankunan za su yi hasarar kudade masu dimbin yawa a karkashin yarjejeniyar kasashen Turai domin farfado da bankunan kasar ta Cyprus

Ana sa ran a yau Assabar mahukuntan kasar Cyprus za su bayyana sabon tsarin ajiyar kudi a bankunan inda masu ajiya sama da euro 100,000 za su samu kaso na kashi 37.5 amma sauran kudadensu za su tafi ne ga bankunan kamar yadda wata majiya ta kwarmatawa kamfanin dillacin labaran Reuters.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.