Isa ga babban shafi
Faransa

Alkalan Faransa za su fadada bincike kan masu boye kudade a waje

Bangaren shari’a na kasar Faransa zai fadada binciken da ya ke gudanarwa a kan tsohon ministan kasafin kudi na kasar Jerome Cahuzac wanda ake zargi da boye dukiyarsa a wajen kasar zuwa ga sauran manyan jami’ai na kasar da ake zargin cewa su ma sun yi irin wannan hali.

Shugaban Faransa, Francois Hollande da tsohon ministansa na kasafin kudi, Jerome Cahuzac
Shugaban Faransa, Francois Hollande da tsohon ministansa na kasafin kudi, Jerome Cahuzac REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Jaridar Le Monde da ake bugawa a kasar ta ce daukar wannan mataki, ya biyo bayan alkalai masu binciken tsohon ministan na kasafin kudi ya gana da wani ma’aikacin wata cibiyar kudade da ke kasar Suisse mai suna Reyl et Cie kasar da ake zargin cewa a can ne ministan na Faransa ya boye kudadensa.
Jaridar ta Le Monde ta bayyana cewa da farko alkalai masu bincike sun gayyaci Pierre Condamin-Gerbier domin ya bayar da shaida dangane da asusun ajiyar Jerome Cahuzac, kuma bayanansa ne suka kara share fage ga irin binciken da suke gudanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.