Isa ga babban shafi
Switzerland

'Yan sanda sun cafke masu zanga-zanga da dama a Switzerland

‘Yan sanda a birnin Berne da ke kasar Suisse, sun ce yanzu haka suna tsare da mutane 61 da suka kama sakamakon tarzomar da ta barke a lokacin wasu bukukuwa masu nasaba da siyasa da aka gudanar a birnin.

Wani titi a kasar Suisse.
Wani titi a kasar Suisse. Thomas Stankiewicz/gettyimages.fr
Talla

Rahotanni sun ce a lokacin wannan tarzoma ta yau lahadi, akalla ‘yan sanda 21 ne suka samu raunuka, kuma rikicin ya barke ne a daidai lokacin da masu zanga-zangar suka yi kokarin karya shingayen da jami’an tsaro suka kafa, yayin da wasu daga cikinsu suka soma jifar ‘yan sandar da kwalaben da aka makare da man fetur sannan kuma aka cinna masu wuta.

Akalla dai mutane dubu 10 ne suka shiga wannan maci, wanda ga al’ada ake shiryawa kusan kowace shekara ba tare da an samu tashe-tashen hankula ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.