Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta dauki matakan kula da tsofaffin ma'aikata

Hukumomin kasar Faransa, sun dau alkawalin aiwatar da sauye-sauyen dangane da batun tsoffin ma’aikata da suka yi ritaya.Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kungiyar tarayyar Turai ta AU, ta bukaci membobin ta, su samar da sauyi kan batun.Hukumar ta bukacin hukumomin na Faransa da su sake aiwatar da sabin dokokin dangane da batun tsofin ma’aikata masu ritaya a kasar, wata dama ta kawo saukin kan batun yawan marasa aiki yi, da matsallar tattalin arziki da kasashen Faransa dama Spain ke fuskanta a yanzu hakka. Batun tsofin ma’aikata masu ritaya a Faransa, na daya daga cikin abubunwan da ya fi jan hankali hukumomi, fiye da shekaru goma da suka gabata.Gwamnatin Shugaba Francois Hollande na ci gaba da tantace hanyoyi, domin shawo kan wanan matsala ba tare da an taka hakin wani ma’aikacin ba.Shugaban Hukumar kungiyar nahiyar Turai Jose Manuel Barroso yace ba za a ciman manufofin da aka sa a gaba, sai an kau da so rai aBarroso ya kara da bayana matsayin da kungiyar ta Nahiyar Turai ta cimma dangane da batun kawo karshen yawan marasa aikin yi a yanki da kuma samarwa mutanen yanki na Turai kayakin more rayuwa.Wani bicinke da hukumar ta gudanar na nuna cewa kasashe 20, daga cikin 27 dake cikin kungiyar ne za su sake aiwatar da sabin dokokin dangane da batun tsofin ma’aikata ma su ritaya.PM kasar Faransa Jean Marc ya jadada aniyar hukumomin kasar Faransa na bin umurni hukumar kungiyar Nahiyar Turai tare da yi amfani da dokar Faransa domin kaucewa duk wata hanya dake iya haifar da zanga-zanga.  

Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban Faransa François Hollande Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.