Isa ga babban shafi
Faransa

An daura Auren farko na jinsi daya a kasar Faransa.

Wani lokaci a yau dinnan ne aka gudanar da Bukin farko na Auren jinsi daya da Dokar kasar Faransa ta amince da shi, bayan share Watanni ana zanga-zangar nuna kyamar Dokar a kasar ta faransa, yanzu dai Auren jinsi daya ya halatta a bisa okar kasar Faransa

REUTERS
Talla

Mutum biyu da suka bada kansu a fara daurawa Auren jinsi daya a kasar ta Faransa sune Vincent da Bruno da ke cike da farin cikin zama na farko ga wannan sabgar.

Daruruwan masu goyon bayan Auren jinsin daya da suka hada da Mata da Maza kazalika da ‘yan Jarida ne suka halarci wannan bukin da aka gudanar.

Magajiyar kudancin birnin Montpellier Helene Mandroux ta bayyana kasancewar wadannan Mazajen biyu a matsayin masu aurar juna.

A ranar 18 ga Watan Mayu ne Majalisar kasar Faransa ta amince da Dokar halasta Auren jinsi daya, matakin da wasu masu bukatar Auren jinsi dayan suka yi farin ciki akai.

Sai dai masu adawa da Dokar da mafi yawancin su Musulmi ne a kasar ta Faransa sun yita gudanar da jerin zanga-zanga domin yiwa kasar ta Faransa Hannunka-mai-Sanda da halin da zata saka kasar sakamaon abinda suka kira babban Bala’in dake shirin sauka sakamakon wannan Dokar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.