Isa ga babban shafi
Spain

Mutanen Spain sun yaba da hukuncin Kotu akan ‘Yar Sarki

A kasar Spain kafafen yada labarai sun yaba da matakin da kotu ta dauka na hukunta Cristina ‘Yar gidan sarkin kasar Juan Carlos bayan zargin ta da badakalar aikata laifin cin hanci da rashawa. Wannan kuma shi ne karo na farko a kasar ta Spain da aka taba samun irin wannan danbarwar da ke da alaka da cin hanci a masarautar

Sarauniya Cristina da Mijinta Inaki Urdangarin
Sarauniya Cristina da Mijinta Inaki Urdangarin REUTERS/Albert Gea
Talla

A bara Mai Shari’a Jose Castro ya taba aikawa Sarauniya mai jiran gado Cristina da sammaci domin amsa zargin cin hanci da rashawa, amma kuma masu shigar da kara suka yi watsi da zargin al’amarin da ya sa kafafen yada labarai a kasar ke zargin ana yin amfani da ikon mahaifinta.

A wannan karon ana ganin da kyar Sarauniyar mai jiran gado zata kai labari domin Alkalin kotun na nuna zai yi adalci game danne kudi miliyan 8 na dalar Amurka da ake zargin sarauniyar da mijinta.

Cikin zarge-zarge da ake wa Cristina akwai kuma hada baki da mijinta wajen wawashe kudin wata kungiya mai zaman kanta da suka kafa sannan kuma suka yi amfani da kudade wajen harkokinsu.

Yanzu dai al’ummar kasar da sauran duniya sun zuba ido domin ganin yadda zata kaya a wannan shari’ar tare da yadda masarautar zata tsira da mutuncinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.