Isa ga babban shafi
Amurka-Spain

Amurka ta nadi Zantukan Miliyoyan mutanen Spain

Kafafofin yada labaran kasar Spain sun ce Jami’an leken asirin Amurka sun nadi zantukan mutanen kasar kusan Miliyan 60 ta wayoyinsu na Salula, kuma wannan ya fito ne daga jami’in leken asirin Amurka Edward Snowden wanda ke aikin fallasa sirrin kasar.

Shugaban Amurka Barak Obama
Shugaban Amurka Barak Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

Rahoton yace Amurka ta kwashi Lambobin mutane da yankunan da suke kira tare da wadanda ake magana da su a wayoyin na Salula, sai dai babu bayani game da hirarrakin da Jami’an leken asirin suka saurara.

Wannan kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da wata tawagar Kungiyar kasashen Turai ke shirin kai ziyara Fadar White House domin tattauna matsalar da gwamnatin Obama.

Bayanan leken asirin da Snowden ya kwarmata, yace Amurka ta nadi bayanai da sakwannin mutanen Spain ne tsakanin 10 ga watan Disewmba na 2012 zuwa 8 ga watan Janairun bana.

Tuni gwamnatin kasar Spain ta gayyaci Jekadan Amurka a Madrid domin ya gana da Ministan harakokin wajen kasar domin su tattauna badakalar leken asirin mutanen na Spain.

Irin wannan ne ya shafi gwamnatin kasar Jamus inda Angela Merkel ke koken Amurka ta nadi zantukanta ta Tarho tsawon shekaru 10, Kuma Jaridar Guardian da ke kwarmato irin wadannan bayanan daga Snowden tace Amurka ta nadi zantukan shugabannin kasashen duniya kusan 35.

Masu sharhi kan Diflomasiyar duniya suna ganin hakan kan ya gurgunta huldar da ke tsakanin kasashen Turai da Amurka da hadin kansu wajen yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.