Isa ga babban shafi
EU-Amurka

Kasashen Turai sun shiga damuwa game da Amurka

Shugabannin Kasashen Turai sun bukaci gudanar da wani taro da Amurka don warware matsalar leken asirin da suke zargin gwamnatin Obama na yi akansu. Wannan kuma ya biyo bayan zargin da shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi akan zantukanta da Jam’in leken asirin Amurka suka saurara.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana rike da wayar Tarho ta hannu.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana rike da wayar Tarho ta hannu. REUTERS
Talla

A Tsokacin da Merkel ta yi dangane da wannan batu, ta bayyana cewa yin leken asiri akan wani amini, wani abu ne da ba za a taba amincewa da shi ba.

Merkel ta ce akwai bukatar kara samun yarda a tsakanin juna, yayin da wata sanarwa da gwamnatin kasar ta Jamus ta fitar a yammacin jiya ke cewa matukar dai wannan batu ya tabbata a matsayin gaskiya, to wannan na nufin yankewar amana a tsakanin Jamus da Amurka.

Mai Magana da yawun fadar shugaban Amurka Jay Carney wanda ke gabatar da taron manema labarai a jiyan, ya ki yin tsokaci a game da wannan zargi da ake yi wa kasarsa na sauraron zantukan wayar shugabar Gwamnatin Jamus, inda ya ce ba zai ce uffan ba a game da zarge-zargen da suka samo tushe daga kalamai irin na bainar jama’a, sai dai manazarta na kallon hakan a matsayin yarda da aikata leken asiri akan Merkel.

Wannan batu ne na leken asiri ya mamaye taron Shugabannin kasashen Turai a birnin Brussels a jiya alhamis inda suka bayyana cikakken goyon bayansu ga kasar Jamus da kuma Faransa, wadanda a yau suka fahimci cewa ashe suna dab da fadawa tarkon leken asirin Amurka.

Wani Rahoto ya bayyana cewar jami’an Amurka sun saurari bayanan wayar tarhon shugabanin kasashen duniya 35 ba tare da sanin su ba.

Jaridar Guardian ta kwarmata cewar, fadar shugaban Amurka, da ma’aikatar tsaron kasar da harkokin waje suka bayar da lambobin shugabanin ga jami’ansu domin sauraron bayanan a asirance.

Rahotan yace, wani babban jami’in Amurka ya bai wa ma’aikatan lambobin mutane 200 da za’a saurari hirarrakinsu, cikin su har da shugabanin kasashen duniya.

Wannan dai ya cusa shakku da dubban mutanen Turai game da wannan batu day a keta hakkinsu na sirrin rayuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.