Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Ukraine ta zargi Rasha da aika dakaru a cikin kasarta

Gwamnatin Kasar Ukraine tace yanzu haka sojojin kasar Rasha 10,000 suka shiga gabashin kasar da ke fama da tashin hankali. Kwamnadan sojin kasar Viktor Muzhenko wanda ya bayyana haka y ace Rasha ta kuma aje sojoji kusan 50,000 kusa da kan iyakar kasar tare da muggan makamai.

'Yan tawayen Ukraine da ke fada da gwamnatin kasar
'Yan tawayen Ukraine da ke fada da gwamnatin kasar REUTERS
Talla

‘Yan Tawayen Ukraine sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar amma har yanzu ana ci gaba da kai hare hare a Yankin.

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama yace zai sanya hannu kan sabbin takunkumin da kasar za ta dorawa kasar Rasha duk da ya ke bai amince da wasu daga cikinsu ba.

Kasar Rasha na fama da matsalar tattalin arziki sakamakon takunkumin da kasashen Yammacin duniya suka kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.