Isa ga babban shafi
Britain

Sarauniya Ta Sami Tattaba kunne Jinjira Mai Jiran Gado

Tun a jiya ne dai , Kate, matar Yarima Williams na gidan sarautar Britaniya ta haifi ‘ya mace wadda ta kasance ta hudu a jerin masu jiran hawa kujeran sarautar kasar Britaniya.Nakuda da haihuwan jinjiran bai dauki wani dogon lokaci ba, Yarima Willian wanda shine jikan Sarauniya Elizabeth ne ya dauko matarsa Kate da jinjiran cikin mota daga asibiti zuwa gida.Tuni dai aka sanar da Sarauniya  Elizabeth  da sauran wadan da suka dace su fara sanin haihuwan kafin a sanar da duniya.Gobe littini za'a yi wani buki na harba bindigogi sama domin murnar samun wannan jinjira da ake shirin sanar da duniya sunan ta.Dubban mutane dai sunyi farin cikin jin wannan haihuwa, inda wasu ke tuna irin farin jinin Gimbiya Diana kakar jinjiran, wadda ta mutu a shekara ta 1997 a wani hatsarin mota a Paris na kasar Faransa.  

Yarima Williams da matar sa Kate da jinjira jim kadan bayan sallamar su daga asibitin St Mary dake London a jiya Asabar 2 mayu 2015.
Yarima Williams da matar sa Kate da jinjira jim kadan bayan sallamar su daga asibitin St Mary dake London a jiya Asabar 2 mayu 2015. REUTERS/Suzanne Plunkett
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.