Firayi ministan Faransa, ya rufe zaman taron jam'iyar Socialist da jawabi mai karfi
A yau lahadi PM kasar Fransa Manuel Valls ya rufe zaman taron jam’iyar Socialist mai mulkin kasar Fransa a birnin La Rochelle da jawabi mai karfi na zage dantse a zabe mai zuwaShidai taron na na tsawon kwanaki uku da jam’iyar ta Socialist ta gudanar, hankalin mahalartansa ya karkata ne a kan kasassabar da ministan tattalin arzikin kasar Emmanuel Macron ya yi ne, kan awowi 36 na lokutan aiki a kasar
Wallafawa ranar:
A cikin jawabin rufe zaman taron Manuel Valls, ya yi kokarin saita agogan ‘yan jam’iyar ta Socialist , inda ya bukacesu, da su amince da banbance banbance dake tsakaninsu
Har ila yau Faryi Ministan Faransa, Manuel Valla ya yi fatan ganin magoya bayan jam’iyar ta yan , sun kara zage dantse wajen tunkarar zaben yankunan kasar da za a yi a cikin watan December wannan shekara ta 2015
Kusurwar da kuma yake fatan ganin magoya bayan, su tunkari, ita ce wajen yin gumurzu a zaben mai zuwa, su kuma san nauyin da ya rataya a wuyansu, tare da kara mayar da hankali da kwazo, da kuma hakkuri da juna, wanda a cewarsa sai da haka zasu iya tunkarar adawar da suke fuskanta daga jam’iyun hamayyar a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu