Isa ga babban shafi
Faransa

Ministan kwadagon Faransa zai sauka daga mukaminsa

Ministan kwadagon Faransa Francois Rebsamen zai sauka daga mukaminsa domin kasancewa sabon magajin garin Dijon, abin da zai tilasta wa shugaba Francois Hollande neman wanda zai maye gurbinsa a daidai lokacin da kasar ke fama da milyoyin masu zaman kashe wando.

François Rebsamen, ministan kwadagon Faransa.
François Rebsamen, ministan kwadagon Faransa. RFI
Talla

Rebsamen ya shaida wa jaridar Le Parisien cewa a ranar 19 ga wannan wata na agusta ne zai mika takardarsa ta murabus bayan kammala taron majalisar ministocin kasar.

Ministan ya ce ba zai iya rike mukamai biyu a lokaci daya ba, saboda haka ya zabi ya sauka daga kujerarsa ta minista sannan ya karbi ma’aikatar magajin garin Dijon.

Matsalar rashin aikin yi dai ta yi kamari a Faransa, inda ta karu da kusan kashi 10 cikin dari, lamarin da kuma ke matsayin barazana ga shugaba Hollande wanda ke fatar sake tsayawa neman shugabacin kasar a shekara ta 2017.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.