Isa ga babban shafi
Faransa

Za mu samu wanda zai saye jiragenmu- Hollande

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce kasar ba ta fuskantar wata matsala wajen samun wadanda za su saye katafaren jiragen ruwan da kasar ta kerawa Rasha da ke daukar jiragen saman yaki amma ta soke cinikin saboda rikicin Ukraine.

Shugaban Faransa François Hollande.
Shugaban Faransa François Hollande. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a kasar Masar lokacin da ya halarci bikin kaddamar da fadada mashigin ruwan Suez a garin Ismailiya.

Kasar Rasha ta bayar da odar a kera mata jiragen ruwan guda biyu akan kudi Dala biliyan daya da miliyan 300 amma sai Faransa ta soke kwangilar saboda matsin lambar kasar Amurka da wasu kasashen Turai kan rawar da Rasha ke taka wa a rikicin kasar Ukraine.

Shugabannin kasashen biyu sun amince da soke cinikin ranar laraba, inda nan take ministan tsaro Jean Yves Le Drian yace wasu kasashen duniya sun bayyana aniyar su ta sayen jiragen.

Masana na ganin dole sai Faransa ta karya farashin jiragen kafin ta sayar da su yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.