Faransa ta soke kwangilar jirage tsakaninta da Rasha
Fadar Shugaban Faransa Francois Hollande ta ce shugaban ya cim ma yarjejeniya da takwaransa na Rasha Vladimir Putin kan biyan diyya sakamakon rashin mikawa kasar jiragen ruwan daukar makaman yaki da ta saya da aka kasa ba ta saboda rikicin kasar Ukraine.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaban Faransa tace za a mayarwa Rasha da kudin da ta biya Dala biliyan daya da miliyan 300 na Jiragen ruwan guda biyu masu daukar jiragen yaki masu saukar ungulu. Sannan Faransa za ta rike jiragen.
Rasha tace tuni Faransa ta mayar da kudaden, bayan shugabannin kasahsen biyu sun cim ma yarjejeniyar soke kwangilar sayen jiragen.
Faransa ta soke kwangilar ne saboda Takunkumin da kasashen yammaci suka kakabawa Rasha kan zargin rawar da ta ke takawa a rikicin Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu